1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sami karuwar masu mutuwa da Corona a Brazil

Binta Aliyu Zurmi
June 10, 2020

An ba da rahoton cewar a cikin sao'i 24 mutane dubu 1272 sun mutu da cutar corona a kasar Barazil wanda addadin kawo yanzu na wadanda suka mutun ya kai mutum dubu 38.406

https://p.dw.com/p/3dYUm
Brasilien Coronaviurs in Rio de Janeiro | Friedhof
Hoto: Reuters/R. Moraes

Yayin da addadin  sabbin mutanen da suka kamu da ciwon ya kai dubu 32.091 addadin da shi ne mafi girma da aka samu tun lokacin da annobar corona ta barke. Kwararu na cewar addadin zai iya ninkawa har sau 15 saboda rashin tatance masu fama da ciwon a kasar ta Barail da ke da yawan al umma miliyan dari 210. Can kuwa a Amirka a halin da ake ciki wani sabon rahoton da jami'ar John Hopkins ta bayyana ya nuna cewar mutane 819 suka mutu da cutar ta corona a cikin kwana guda.