Brazil: Binciken cin hanci ga tsohon shugaba Lula da Silva
May 11, 2017Sai dai tsohon shugaban mai shekaru 71 da haihuwa, bayan ya amsa tambayoyin ya fuskanci dumbun magoya bayanshi, inda ya yi watsi da zargin da ake yi masa:
"Ban taba neman a bani ba, kuma ban tama karbar wani gida ba kaman yadda ake zargina da shi, na zo gaban kotu ne don yin biyayya ga dokokin da kundin tsarin mulkinmu ya tanada, amma kuma ina mai yi wa wannan shari'a kallon wata manakisa."
Sai nan da zuwa 'yan makonni ne za a iya sanin makomar tsohon shugaban kasar ta Brazil dangane da wannan shari'a, inda ake zargin ya karbi toshiyar baki daga wani kanfanin gine-gine da ake zargin ya bai wa tshon shugaban wani gida a matsayin cin hanci a lokacin yana shugabancin kasar ta Brazil, wanda idan har aka same shi da laifi, to hakan zai dusashe burin da yake da shi na sake dawowa kan karagar mulkin kasar.