1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brahimi zai maye gurbin Annan a Siriya

August 17, 2012

Majalisar Ɗunkin Duniya ta tabbatar da cewar, sabon jakadan na ta a Siriya, ya na da nashi salon yadda zai fuskanci rikicin.

https://p.dw.com/p/15s90
Diplomat Lakhdar Brahimi speaks with former U.S. President Jimmy Carter (not pictured) during a joint news conference in Khartoum in this May 27, 2012 file photo. Veteran Algerian diplomat Brahimi is expected to be named to replace Kofi Annan as the U.N.-Arab League joint special envoy for Syria barring a last-minute change, diplomats said on August 10, 2012. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah/Files (SUDAN - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Tsohon jami'in diplomasiyyan ƙasar Algeria Lakhdar Brahimi, ya amince da maye gurbin Kofi Annan, a matsayin mai shiga tsakani na ƙasa da ƙasa wajen yunƙurin warware rikicin ƙasar Siriya. Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban ki-moon da shugaban ƙungiyar ƙasashen larabawa Nabil Elaraby ne, suka sanar da amincewar Brahima mai shekaru 78 da haihuwa. Majiyar na nuni da cewar, sabon jakadan na da nashi tsarin da zai bi, wajen tunkarar rikicin na watanni 17, da sannu a hankali yake rikiɗewa zuwa yaƙin basasa. A ƙarshen watan Augustan nan ne dai tsohon sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, yake ajiye mukaminsa na shiga tsakani, bayan watanni shida. Kofi Annan yace yunƙurin shi na samar da zaman lafiya a Siriya, ya fuskanci cikas daga rarrabuwar kawuna daya dabaibaye komitin sulhun Majalisar Ɗunkin Duniyar. Fadar gwamnatin Amurka ta white house dai ta bukaci Majalisar data yi bayanin ayyukan sabon jakada Brahimi a Siriya, duk da cewar ta bayyana shi da kasancewa kwararre.

Rahotanni daga siriyan dai na nuni da cewar, ana ci gaba da gwabza fada tsakanin 'yan tawaye da sojojin Bashar al-Assad, batu da ake ganin zai iya zama mawuyaci a yunkurin gano bakin zaren warware rikicin Siriyar.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman