Brahimi ya gana da 'yan adawar Siriya
September 14, 2012Manzon musamman na kasa da kasa domin samar da zaman lafiya Siriya Lakhdar Brahimi ya gana da 'yan adawa a sabon yunkurin da yace na wanzar da zaman lafiya. kakakin 'yan adawan Hassan Abdel Azim yace sun baiyanawa jakadan na musamman cewa a shirye suke su bada hadin kai domin kawo karshen hasarar rayuka tare da samar da magunguna wadanda suka jikata da kuma ganin an sako fursunonin siyasa da ake tsare da su. Brahimi wanda ke ziyararsa ta farko a Damascus tun bayan nada shi mai shiga tsakani don kawo karshen rikicin Siriya zai gana da bangorin 'yan adawa da kuma gwamnati inda tuni ya sadu da ministan harkokin wajen Syria Walid Mualem. Ana kuma sa ran zai gana da shugaba Bashar al-Assad a ranar Asabar din nan.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe