1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata a fannin tuka jirgin sama a Botswana

February 26, 2020

A kasar Botswana wata matashiya ta bullo da tsarin da zai kara wa mata azama wurin shiga a dama da su a fannin tuka jirgin sama.

https://p.dw.com/p/3YTjg
Symbolbild Flugzeug Beechcraft
Hoto: Getty Images/AFP/P. Pavani

Matashiya Kgomotso Phatsima mai tuka jirgin sama a cikin wani jirgin. Shekaru goma da suka gabata ta kammala samun horon tukin jirgin sama a kwalejin horas da sojoji ta Botswana. A cikin gida Botswana matashiyar ta shahara a wannan fanni, ta kuma sami kyaututtuka daga ciki da wajen kasarta. Kawo yanzu ta kafa kungiya mai suna Dare to Dream domin koyar da mata matasa tukin jirgin sama da sauran ayyukan da ke da nasaba da kimiyya da fasaha da ake ganin maza sun mamaye.

''A lokacin da nake tasowa ban samu damar zama kusa da matukin jirgin sama ko shiga cikin jirgi ba. Sai daga baya lokacin da na samu horo na musamman. Hakan ne ya sa na ce to bari in kafa abin da zai taimaki al'umma kuma ya karfafa gwiwar matasa da ke kauyuka su zama kamar yadda nake a yau. Ta haka ne na fito na yi wannan hobbasa.''

Kungiyar Phatsima ta Dare to Dream ta yi fice a kan shirinta na koya wa matasa tukin jirgin sama ta hanyar amfani da na'urar da ke a wuri guda kafin daga bisani su fara tunanin shiga cikin jirgin sama a zahiri. Sun yi hadin gwiwa da jami'ar Botswana inda suka gudanar da wata gasar shawagi ta jirgin sama. A yanzu matasa maza da 'yan mata guda 250,000 suka amfana.

''A shekarar da ta gabata mun koya wa dalibai 2000 wannan aiki. Mun zabo su daga yankunan karkara da birane mun bayar da karfi sosai a kan koya musu harkar jirgin sama. A bana, kamfanin Airbus zai zo Botswana kuma za mu hada hannu wurin koyar da dalibai 2000 dabarun tukin jirgin sama, da tauraron dan Adam da sauran abubuwa makamantan haka.''

Rathabile Mphafe na cikin daliban da shirin kungiyar kungiyar kyaftin Phatsima ya taimake su. A saboda kaifin basirar Mphafe daga karshe sai ta shiga cikin matasa da ke aiki a kungiyar kyaftin Phatsima don ci gaba da taimakon mata.

"Mun fara haduwa da matukiyar jirgin saman Phatsima a shekarun baya lokacin tana koya mana darasin lissafi a sakandare. A lokacin gaskiya ba na gane darasin lissafi amma daga bisani ta janyo ni kusa har tana shirya min darasi ni kadai a kan lissafin. A karshe sai ga shi na gama makaranta da sakamako mai kyau. Shekaru takwas ke nan da Phatsima ta bukaci in zama sakatariyarta a kungiyarta."

Duk da irin wannan ci-gaba da ake samu dai, matashiyar mai tuka jirgin saman, Phatsima ba ta gamsu da yadda ta ce fararen fata da maza ke ci gaba da yin kaka-gida a bangaren sufurin jiragen sama ba. A kan haka ta ajiye aikinta a rundunar sojin Botswana don ta zo ta ci gaba da karfafa wa mata gwiwa don su shiga a dama da su a wannan fanni.