1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren yin Allah wadarai da tsadar rayuwa a Sudan

June 22, 2012

Mutane da dama sun gudanar da zanga-zanga a wasu sasaa na kasar sudan domin yin Allah wadai da hauhawar farashin kayan bukatun yau da kullum a kasuwannin kasar.

https://p.dw.com/p/15K4v
--- 2012_03_27_sudan_südsudan_englisch.psd

Daruruwan mutane sun ci gaba da gudanar da zanga zanga a wasu sassa na kasar Sudan, domin nuna rashin jin dadinsu game da hauhauwar farashin kayan bukatun yau da kullum a kasuwanni. Wannan bore da dalibai suka fara shi tun kwanaki bakwai da suka gabata, ya bazu i zuwa unguwar masu hannu da shunu da kuma ofisoshin jakadanci kasashen waje da ke khartum. A Omdurman da ke daya bangare na babban birnin ma dai, kimanin mutane 200 suka yi kone konen tayoyi, tare a harbin 'yan sanda da duwatsu.

 Sai dai jami'an na tsaro sun yi amfani da borkono mai sa hawaye da kulake wajen tarwatsa masu zanga-zangar. A wasu unuguwanni na Khartum dai ciki kuwa har da Burri, 'yan sanda sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa zanga-zangar. Haka lamarin ma ya kasance a birnin Sennar da ke kudancin Sudan idan mutane 300 suka nuna kosawa da mawuyacin hali da suka shiga sakamakon tsadar rayuwa.

Bisa ga alkaluma da gwamnati sudan ta fitar dai, karin kashi 30 daga cikin 100 na farashin aka samu a watannin baya-bayannan akan matsarufi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar