1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Nijar na son raba gari da Faransa

Abdoulaye Mamane Amadou Muntaqa Ahiwa
September 2, 2023

Dubban magoya bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, sun gudanar da zanga-zangar kin jinin sojin Faransa a babban birnin Niamey a wannan Asabr.

https://p.dw.com/p/4VsvK
Niamey I Niger I Masu zanga-zanga I Kin jinon sojan Faransa
Niamey I Niger I Masu zanga-zanga I Kin jinon sojan Faransa Hoto: Stringer/Reuters

Masu boren na son ne ko ta halin kaka sojojin Faransa su tattara nasu-ya-nasu su fita daga kasar, kamar yadda jagororin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum suka bukata.

Hadin gwiwar wasu kungiyoyin fararen hula ne dai suka kira gangamin, da aka yi a kusa da sansanin sojojin Faransa a Nijar, dauke da alluna masu zafafen kalamu ga kasar da ta yi wa Nijar mulkin mallaka, masu boren sun yi ta nuna adawarsu ta kasancewar Faransa a wannan kasa.

Karin Bayani: Nijar na tankiya da Faransa

A farkon wannan makon ne kasashen biyu na Faransa da Nijar suka shiga zaman doya da manja, bayan da gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta kori jakadan Faransa bisa zargin kasancewarsa a wannan kasa ka iya hadasa fitina, matakin da Faransar ta yi fatali da shi tana mai cewar sojojin ba sa da wani hurumi na korar jakadanta.

Duk da matakin doka da gwamnatin mulkin sojin Nijar ta dauka na korar jakadan Faransa, yarjejeniyar Vienna ta Diflomasiyya ta haramta duk wani jam'in tsaron kasar da jakadan wata kasa yake kutsawa a ciki ba tare da hurumin wannan kasa ba.