1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren adawa da ƙungiyar NATO

May 21, 2012

Jami'an tsaro sun tsare mutane da dama dake yin Allah wadai da ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO

https://p.dw.com/p/14zAk
Die Staatsfuehrer und Aussenminister der Mitgliedsstaaten der NATO stehen am Sonntag (20.05.12) in Chicago (Vereinigte Staaten) bei der ersten Arbeitssitzung des NATO-Gipfels an ihren Plaetzen, waehrend Soldaten der Mitgliedsstaaten eine Zeremonie durchfuehren. Spitzenvertreter von mehr als 60 Laendern und internationalen Organisationen berieten den Abzug der Kampftruppen aus Afghanistan bis Ende 2014 und die kollektive Verteidigung in Zeiten der Schuldenkrise. (zu dapd-Text) Foto: Michael Gottschalk/dapd.
Taron NATO a birnin ChicagoHoto: dapd

A yayin da shugabanni ke ganawa a cikin babbar cibiyar gudanar da taro na birnin Chikagon ƙasar Amirka, 'yan sanda sun yi taho mu gama tare da masu zanga zanga a wajen cibiyar, wadda ke zama dandalin taron yini biyu na ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO. Wannan matakin ya zo ne bayan da jami'an 'yan sanda sun umarci masu zanga zangar da ko dai su watse ko kuma su fuskanci hatsarin cafke su. Ko da shike akwai masu boren da suka watse, amma dai ɗaruruwan masu zanga zangar ne suka yi watsi da wannan umarnin.

Wata ƙungiyar lauyoyin dake wakiltar masu zanga zangar tace fiye da mutane 60 ne aka tsare, kana aƙalla mutane 12 ne kuma suka sami rauni, wasun su ma a kawunan su. Sai dai kuma jami'an 'yan sanda basu kai ga fitar da alƙalumar adadin waɗanda suka tsare ko kuma na waɗanda suka sami raunin ba. Daga bisani dai titin da shugabannin ƙungiyar ƙawancen tsaron NATOn ke gudanar da taron nasu yayi tsit.

A halin da ake ciki kuma shugaban Afghanistan Hamid Karzai da taron NATO ke mayar da hankali akan batun janyewar dakarun ƙetare daga cikin ƙasar sa, yace a shirye suke su sauke nauyin daya rataya a wuyansu:

"Ya ce Afghanistan na jaddada ƙudirin ta game da shirin janye dakarun ƙetare daga ƙasar, wanda kuma ke kammala a shekara ta 2014, ta yanda ƙasar ta Afghanistan ba za ta ci gaba da zama wani nauyi bane akan sojojin ƙawayenta da kuma al'ummomin ƙasa da ƙasa."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe