1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren adawa da tsadar rayuwa a Burkina Faso

April 19, 2011

Shugaba Blaise Campaore na Burkina Faso ya naɗa jakadan ƙasar a Faransa a matsayin sabon firaministan - a dai dai lokacin da ɗaliban makarantu da jami'an 'yan sanda suka bi sahun sojoji wajen boren ƙyamar tsadar rayuwa

https://p.dw.com/p/10wbJ
Hoto: AP

Ɗalibai a ƙasar Burkina Faso sun shiga a dama dasu cikin zanga-zangar nuna adawa da tashin farashin kayayyakin abincin da sojojin ƙasar suka fara, kana jami'an 'yan sanda suka rufa musu baya, lamarin daya sa tashin hankalin da ake fuskanta a Ouagadougou babban birnin ƙasar yaɗuwa zuwa wasu manyan biranen ƙasar guda huɗu.

Wannan dai shi ne karon farkon da jami'an 'yan sanda ke cikin boren nuna adawa da tsadar rayuwar tun bayan fara shi a ranar Alhamis da ta gabata, bisa dalilin da wani jami'i ya ce suna neman a biya su albashi ne, wanda ya kamata su karɓa a ranar wannan Litinin.

Mazauna garin Kaya dake yankin arewacin ƙasar suka ce sojoji da kuma wasu jami'an tsaro sun yi ta harbi a iska, wanda kuma ya yi sanadiyyar ƙonewar gidan wani babban jami'in soji, baya ga binciken da suka yiwa gidan wani jami'in dake yankin, abinda yasa garin na Kaya ya zama na huɗun da ya fuskanci rikicin, baya ga biranen Ouagadougou da Po da kuma Tenkodogo dake kudancin ƙasar.

A can yammacin ƙasar kuwa boren da matasa a birnin Koudougou suka yi ya rikiɗe zuwa tashin hankalin daya kai ga ƙona ofishin jam'iyyar dake mulki ne, abinda a cewar Erman Yameyogo, shugaban jam'iyar adawa ta ÜNdede a ƙasar Burkina faso akwai darasin daya kamata shugabannin su koya daga matakin da matasan suka ɗauka:

"ƙona ma'aikatun gwamnati da kuma cibiyar jam'iyar CDP da ke mulki, kukan kurciya ne ga waɗanda ke riƙe da madafun iko. Wannan na nuna irin ƙaurin suna da shugabanni suka yi a idanun jama'a. Shi ya sa muke gani, ba wai tsayawa za a yi a matakin matsa wa Blaise Campaore ya sauka daga karaga ba. Dole ne a raba kakakin majalisa da ma manyan hapsoshin sojoji da muƙamansu. Ba za a cimma wannan burin ba, sai idan an samar da sabon kundi da zai bayar da damar kafa sabuwar jamhuriyya."

Baya ga ofishin jam'iyyar dake mulkin da matasan Burkina Faso suka ƙona, sun kuma cinna wuta ga gidan tsohon firaministan ƙasar Tertius Zongon da shugaba Campoare ya sallama a ranar Jumma'ar da ta gabata, kana ya maye gurbin sa da jakadan ƙasar a Faransa wato Luc-Adolphe Tiao a matsayin sabon firaminista da yammacin Litinin ɗin nan.

A halin da ake ciki kuma wata majiya daga Burkina Faso ta bayyana cewar hukumomin ƙasar sun fara biyan kuɗaɗen alawus-alawus a barikokin sojojin ƙasar, wanda ke zama ɗaya daga cikin muhimman buƙatun dakarun dake boren, yayin da a ɗaya hannun kuma gwamnatin ke yin ƙira samun kwanciyar hankali a ƙasar.

A cikin wata sanarwar da kakakin sojojin dake gadin shugaban ƙasar Moussa Abdoulaye ya karanta - ta tashar telebijin a ƙasar, ya buƙaci 'yan uwansa sojoji su kawo ƙarshen boren da suke yi, bisa la'akari da abinda ya ce ta'adin da matakin ke janyowa fararen hular da ya kamata su kare. Ya kuma jaddada goyon bayan su ga shugaban ƙasar Blaise Campoare, wanda ya ɗauki matakin sallamar shugabannin mayaƙan sama dana ƙasa da kuma da 'yan sanda, tare da rusa majalisar ministocin ƙasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Mohammed Abubakar