1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boren adawa da gwamnatin Siriya na ci gaba da wanzuwa

September 17, 2011

Jami'an tsaron Siriya na ci gaba da yin fito-na-fito da 'yan adawar ƙasardake rajin tabbatar da bin tafarkin dimoƙraɗiyya

https://p.dw.com/p/12bGw
Jerin gwanon adawa da shugaba Assad a ranar 19.07.2011 a birnin DamascusHoto: dapd

Masu fafutuka a ƙasar Siriya sun bayyana cewar ana ci gaba da jin ƙarar fashe-fashen bama bamai da kuma harbe-harben bindigogi a yankin gabashin ƙasar, yini ɗaya kachal bayan da jami'an tsaron ƙasar suka kashe kimanin mutane 50. A cewar Omar Idibi, kakakin wani kwamitin masu fafatukar wanzar da dimoƙraɗiyya a Siriya, dakarun gwamnati suna ƙaddamar da farmaki a yankin al-joura, inda ya ce tuni suka tsare kimanin mutane 20.

A can lardin Daraa kuwa masu zanga-zanga ne suka yi jerin gwanon su akan titunan garin al-Soura, kana jami'an tsaro na ci gaba da tsare jama'a a garin Nimr- kamar yadda masu fafutkar suka sanar a shafin su na yanar gizo. Sun kuma ƙara da cewar mutane da dama ne suka jikkata bayan da jami'an tsaro suka farma masu zanga-zangar a garuruwan Hama da Homs da kuma wasu garuruwan dake wajen Damarcus babban birnin ƙasar ta Siriya.

Kimanin mutane dubu 2,600 ne suka mutu tun bayan da dakarun dake biyayya ga shugaba Bashar al-Assad na Siriya suka fara ɗaukar matakin daƙile masu boren adawa da gwamnati, lamarin daya sanya Amirka da kuma tarayyar Turai sanyawa ƙasar takunkumi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou