1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta sako magajin garin Kabalewa

Gazali Abdou Tasawa MAB
January 5, 2020

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa, kungiyar Boko Haram ta sako magajin garin Kabalewa na Jihar Diffa da mai dakinsa wadanda ta sace a daren 19 ga watan Oktoban da ya gabata a gidansa.

https://p.dw.com/p/3Vjxo
Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

Abari Elhaj Daouda magajin garin Kabalewa ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a wannan Lahadi cewa kungiyar ta Boko Haram ta sako shi ne a jiya Asabar bayan da suka biya kudin fansa kimanin miliyan 20 na CFA kwatankwacin Euro dubu 30 da kungiyar ta bukata.

 Abari Alhaji Daouda ya kara da cewa tun a ranar Talatar da ta gabata ce kungiyar ta sako shi shi da matar tasa a gabar tafkin Chadi. Sai dai kasancewa ruwa sun kawo a cikin tafkin ya sa suka kasa ketarawa zuwa gida, inda daga karshe kungiyar ta Boko Haram da kanta ta nemi kwale-kwale ta ketaru da su.