Boko Haram ta hallaka mutane 7 a Diffa
November 23, 2018A Jihar Diffa da ke Jamhuriyar Nijar, ma'aikata kimanin bakwai ne na wani kamfanin hakar ma'adanai tare da wani jami'in gwamnati suka rasa rayukansu a wani hari da 'yan Boko Haram suka kai lokacin da suke barci a gida.
Harin dai ya haifar da fadamuwa a yankin Diffa da ke makwabtaka da tafkin Chadi bayan samun kwanciyar hankali na dan wani lokaci.
Dukkan mutanen da lamarin ya shafa 'yan Nijar. An kuma harbe su ne a kauyen Toumour da ke iyaka da Najeriya inda suke aikin haka rijiya domin samar da ruwa don inganta rayuwar 'yan gudun hijira da ke zaune a yankin.
Ma'aikatan suna aiki ne da kamfanin Foraco na kasar Faransa wanda ke aikin hakar ma'adanai da kuma rijiyoyin burtsatse.
Wasu mutane biyar sun sami munanan raunuka a kuma garzaya da su asibitin Diffa domin samun magani.
Rahotanni sun ce maharan sun yi awon gaba da motocin kamfanin guda biyu.