1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawarwaki a gidan kason Chadi

Abdoulrazak Garba Babani LMJ
April 20, 2020

Rahotanni daga kasar Chadi na nuni da cewa an samu gawarwakin mayakan Boko Haram 44, a wani gidan kaso da ake tsare da su a kasar Chadi.

https://p.dw.com/p/3bAor
Tschad Armee Soldaten Zeremonie
Gumurzu da Boko Haram a yankin Tafkin ChadiHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Mahukuntan kasar Chadi na gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar mayakan na Boko Haram da ake tsare da su a wannan gidan kason, bayan da sojojin Chadin suka fafata da su a yankin Tafkin Chadi. An dai tsare mayakan 58 da nufin gurfanar da su gaban kuliya, inda 44 cikinsu suka riga mu gidan gaskiya. Mahukuntan na Chadi dai sun ce a gwajin da aka yi wa gawarwaki hudu cikin 44 da suka riga mu gidan gaskiya, an gano cewa sun ci guba ne. 

Tuni dai masu fashin baki da kuma masu rajin kare hakkin dan Adam, suka bayyana rashin jin dadinsu, ganin cewa ana iya samun bayanai daga bakin wadannan mayakan, inda kuma suka sha alwashin cewa suma za su gudanar da bincike a nasu bangaren, domin gano gaskiyar abin da ya halaka mutanen.