1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bobi Wine ya samu kan sa

January 25, 2021

Wata kotu a Yuganda ta zatas da hukuncin dakatar da daurin talalar da ake yi wa Bobi Wine a birnin Kampala wanda sojoji suka yi wa gidan sa zobe tun bayan zaben shugaban kasar da aka yi a rana 14 ga watan Janairu.

https://p.dw.com/p/3oNat
Uganda Wahl Robert Kyagulanyi Bobi Wine
Hoto: Sumy Sadruni/AFP/Getty Images

Bobi Wine dan takara da ya sha kaye a zaben shugaban kasar a gaba Yoweri Musseveni wanda ya samu nasara a karo na shida a zaben shugaban kasar. Gwamnatin Yuganda ta ce ta tsare shi ne a gida, domin hana zanga-zangar 'yan adawar tare a ba shi kariya.

Matsin lamba dai daga kasashen duniya ya sa gwamnatin ta Musseveni saki Bobi wine.