1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bitar ayyukan Kofi Annan a Majalisar Ɗinkin Dunia

November 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bubu
Hoto: AP

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, ya yi bitar ayyukan da ya gudanar a tsawan shekaru 10 da ya jagorancin wannn Majalisa.

Annan, ya gabatar da wannan bita, a yayin da ya rage masa, wata guda kaccal, kamin ya sauka daga wannan muƙami.

Ya kasa bitar gida 2, a kashin farko, ya nunar da nasarorin da aka cimma na kawo ƙarshen tashe-tashen hankulla, a wasu yankun na dunia, mussamman Afrika, ta hanyar diplomatia, ya bada misalin Burundi, Liberia, Siera-leone, da makamantan su.

Sannan ya yaba ƙoƙarin Majalisar Dinkin Dunia, na ci gaba da lalubo hanyoyin warware sauran yaƙe- yaƙe da ke wakana, a dunia kamar na yankin gabas ta tsakiya, da wasu sassa na Afrika.

Saidai, duk da wannan nasarorin da a ka cimma, akwai sauran rinan kaba , inji Koffi Annan,ta la´alari da babban giɓin da ke akwai, ta fannin ci gaba, tsakanin ƙasashe masu tasowa da masu karfin tattalin arziki.