1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya ta yi fatali da batun zama a EU

Mouhamadou Awal Balarabe
March 14, 2019

'Yan majlisar dokokin Birtaniya sun yi watsi da wani kudiri da ya nemi jinkirta ficewar kasar daga cikin Kungiyar Tarayyar Turai domin samun damar sake gudanar da zaben raba gardama na biyu a kan wannan batu.

https://p.dw.com/p/3F56I
UK Unterhaus lehnt zweites Brexit-Referendum ab
Hoto: Reuters TV

'Yan majalisar dokokin Birtaniya 334 sun nuna adawa yayin da 85 suka yi na'am da yunkurin sake tambayar 'yan kasar ko suna so su ci gaba da zama a cikin EU ko kuma raba gari da wannan gamayya. 

Kwanaki 15 ne suka rage Biratniya ta yi sallama da EU a ranar 29 ga watan Maris 2019, amma har yanzu majalisar kasar da ma al'umma na ci gaba da samun sabani a kan hanyoyin ficewa da kuma kan makomar dangantaka tsakanin sassa biyu.

Su dai 'yan majalisar Birtaniya sun ki amincewa da yarjejeniyar da gwamnatin kasar ta cimma da kungiyar Tarayyar Turai don ficewa cikin ruwan sanyi, suna masu nuna adawa da ci gaba da amfani da dokokin kasuwanci na EU.