1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaYemen

Birtaniya za ta shiga kafar wando guda da 'yan Huthi

Abdoulaye Mamane Amadou
January 14, 2024

Birtaniya ta ce a shirye take ta sake mayar da martani mai zafi kan mayakan Huthi, da ke ci gaba da kaddamar da hare-hare ba kakkautawa kan jiragen ruwan dakon kaya na kasa da kasa a Bahr Maliya.

https://p.dw.com/p/4bDt6
Ministan harkokin wajen Birtaniya David Cameron
Ministan harkokin wajen Birtaniya David CameronHoto: Victoria Jones/emipics/picture alliance

A cikin wata mukalarsa da aka wallafa a jaridar Sunday Telegraph, ministan harkokin wajen Birtaniya David Cameron, ya ce a baya kasar ta aike da gaggarumin sako ga mayakan Huthi, kana a shirye take ta sake yin fada da cikawa.

Kalamun ministan harkokin wajen na Birtaniya na zuwa ne, bayan da a wannan Jumma'a Amurka da Birtaniya, suka kaddamar da luguden wuta kan mayakan Huthi masu samun goyon bayan Iran.

Kungiyar Huthi, sun shiga ne kai tsaye a fadan da Isra'ila take yi da Hamas, inda suka lashi takobin kai jerin hare-hare kan jiragen dakon kayan kasa da kasa da ke bi ta tekun Bahar Maliya.