1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure daga Birtaniya zuwa Ruwanda

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
June 14, 2022

Gwamnatin Birtaniya ta kare shirinta mai sarkakiya na fara jigilar bakin haure masu neman mafakar siyasa a kasar zuwa Ruwanda. Tuni dai shugabannin Coci a fadin Ingila, suka bayyana matakin da abun kunya.

https://p.dw.com/p/4Chsz
Birtaniya I Zanga-Zanga I Masu Neman MAfaka I Ruwanda
Daruruwan mutane sun yi zanga-zangar kin amincewa da iza bakin hauren RuwandaHoto: Niklas Halle'n/AFP/ Getty Images

Sakatariyar harkokin waje Liz Truss ta jaddada cewar jirgin farko zuwa Kigali wanda aka dauko hayarsa daga Spain zai tashi cikin dare, ba tare da la'akari da kankantar masu neman mafakar siyasar ba. Ya zuwa yanzu dai mutane bakwai ne kadai za a kai Ruwandan, maimakon 130 da aka ayyana tun farko saboda rashin kammala shari'ar kalubalantar fitar da su daga Ingila. Akwai dai alkaluma da ke nuni da bakin haure masu dimbin yawa da suka shiga Birtaniyan ta cikin ruwa daga yankin arewacin Faransa, lamarin da ya jefa gwamnati a London cikin yanayi na matsin lamba. Wannan batu dai ya tilasta mata daukar mataki, ba ya ga alkawarinta na sake tsananta tsaro a kan iyakokinta bayan ficewarta daga kungiyar Tarayyar Turai EU.

London | Zanga-Zanga
Kungiyoyi masu zaman kansu sun nuna adawarsu da iza keyar masu neman mafakaHoto: Niklas HALLE'N/AFP

An kiyasta cewa sama da mutane dubu 10 ne suka cimma nasarar shiga Birtaniyan cikin kwale-kwale, a wannan shekara da muke ciki kadai. Ita kuwa gwamnatin Ruwanda mai masaukin baki, ta sake kare kanta ne dangane da wannan shiri mai sarkakiya na karbar masu neman mafakar siyasar da aka kora daga Birtaniya. Mahukuntan na KIgali, sun ce a shirye suke tsab, domin yin maraba ga dubban masu neman mafakar da hannu biyu. Birtaniyan dai ta cimma yarjejeniyar dalar Amirka miliyan 148 da Kigali, domin tura mata bakin haren masu neman mafakar siyasar da suka shiga kasar ta barauniyar hanya a kananan kwale-kwale daga wasu kasashen Turai. Majalisar Dinkin Duniya da ma kungiyoyin kare hakkin dan Adam dai sun nuna adawa da wannan yarjejeniya, sai dai mai magana da yawun gwamnatin Kigali Yolande Makolo ta bayyana ta da "shiri mai muhimmanci da aka kirkira".