Birtaniya da Faransa na son rage kwarar bakin haure
November 14, 2022Talla
Ministan cikin gida na Faransa Gerald Darmanin zai karbi bakuncin takwararsa ta Birtaniya Suella Braverma a birnin Paris don sanya hannu kan yarjejeniyar ta kara jami'an da ke rika sintiri a tekunan kasashen.
Birtaniya dai ta ce za ta kara kudin da ta ke bai wa Farasan a duk shekarar zuwa dala miliyan 71 domin magance matsalar.
Alkalumma sun yi nuni da cewa fiye da mutane dubu 40 ne suka yi amfani da kwale-kwale wajen tsallakawa zuwa kasashen Turai a cikin wannan shekarar, lamarin da ya sanya sabon Firanministan Birtaniya Rishi Sunak ke fuskantar matsin lamba don samar da hanyar da za a rage kwarar bakin haure.