1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta hana shiga kasarta

January 6, 2021

China ta dakile yunkurin hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya na kokarin gano asalin cutar Corona.

https://p.dw.com/p/3nYaL
Tedros Adhanom Ghebreyesus, Direktor WHO
Hoto: picture-alliance/dpa/KEYSTONE/S. D. Nolfi

Hukumomin Chaina sun dakatar da kwararrun da Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta tura shiga kasar domin binciken musabbabin annobar Corona.

Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna rashin jin dadinsa kan abin da kasar Sin din ta yi, duk kuwa da cewa sun yi ta da wajewa tsakanin  hukumar da mahukuntan na Beijing.

Cutar ta COVID-19 ta fara bullarta ne a kasar ta China ne a shekara ta 2019, zance da kasar ke cigaba da nuna shakku a kai.