Nijar: Farfado da al'adar Shayi ga yara
June 25, 2019Talla
A wannan karon yara akalla 46 ne aka yaye ta hanyar wani kasaitacen biki bayan zaman kwanaki 14 na jinya a sansani guda. Mai alfarma wazirin Gaffati ne dai ya dauki dawainiyar yara a fannin dan abun asafin aikin shayin da ake bai wanzaman da suka gudanar da baki dayan aikin shayin tare kuma da dinka sababin kaya ga yaran. An dai gudanar da bikin yaye yaran cikin kade-kade da raye-raye a jihar ta Damagaram da ke jamhuriyar Nijar lafiya.