Bikin raya al'adun Afirka a Würzburg na Jamus
Kida, waka, rawa da juya na daga cikin kyawawan al'adun Afirka da aka raya a karo na 31 na babban bikin Turai na al'adun Afirka da ya gudana birnin Würzburg na tarayyar Jamus.
Al'adar Baveriya ta sadu da ta Afirka
Wannan tufa mai suna dirndl ba nuna ainihin tushen Lea mai shekaru 21 kawai take ba, amma kuma tana nuna abin da bikin Afirka a Würzburg yake nufi: Bambancin al'adu, yarda da kauna. Lea na sa ran saka wannan dinkin a bikin Oktoberfest na wannan shekara.
'Taimaka wa harkokin kida daga Jamus'
Bikin da ya fara a shekarar 1989 a karkashin taken "Yunkurin taikama wa harkokin kida daga Jamus" ya zama daya daga cikin muhimman al'amura na kida da al'adun Afirka a Jamus. A cikin shekarun da suka gabata, fiye da mawaka da masu fasaha 7,000 daga kasashen Afirka 56 da kuma na yakin Caribbean sun gabatar da mabambantan al'adu zuwa wannan karamin garin na Jamus.
Bushe-bushe daga Femi Kuti
Tare da nagartaccen sauti daga saxophone da kuma kyakkyawar yanayi, Femi Kuti - da ga Fela Kuti - ya nishadantar da wadanda suka hallara. "Afrika za ta kasance mai girma," in ji shi, a wata waka da ke sukar 'yan siyasa na Afirka.Ya ce "Muna bukatar jagoranci mai kyau, kuma dole dukkan 'yan Afirka su shiga a dama da su,"in ji Kuti, "Matasa sun fahimci cewa rayuwarsu ce kuma suna bukatar adalci."
Salon kida na soul
Wani salon kida kuma shi ne na Ndlovu Youth Choir daga Afirka ta Kudu. Abin da ya fara shekaru goma da suka wuce a matsayin aikin da zai taimaka wa matasa masu fama da talauci ya rikide zuwa na hadin kai. Sun sha yabo daga sassa na duniya a shekara ta 2018 bisa wakarsu mai taken "Shape of You" na Ed Sheeran da aka rera cikin harshen Zulu.
Kora ta hadu da salon kida na zamani
Wannan abin kida na kora da ake samu a yammacin Afirka sun hada da na soul. Mawaki na kasar Senegal mai suna Saliou Cissokho ya fito ne daga tsatson maroka - masu kida da waka na gargajiya. Tare da matarsa, Anna, ya surka salon kida na kasar Senegal da kida na zamani. "Kasancewa a nan ya kasance abu na musamman. Mu duka dangi daya ne." In ji shi.
Al'adun Karibiyan a Baveriya
Shiga irin ta al'ada tare da makada da kuma masu rawan samba ya kawo wa bikin wata tsaraba daga yankin Karibiyan. Shahararrun makadan sun fito ne daga Aruba da Curacao, tsibirai guda biyu na bakin tekun Kudancin Amirka. Wakar da rawa da suka fito daga can sun daga bayin Afirka da aka kawo dada daya bangaren na Atlantkac. Bikin al'adun ya kasance hadi tsakanin al'adun da abin da zamani ya kawo.
'Launi dabam-dabam - mutane daya'
Wannan shine maudu'in bikin na wannan shekara, kuma mawaka da makada da 'yan kallo sun rungumeshi hannu bi-biyu. "Aikin Afirka na sada zumunci kuma yana kawo kaunar al'adun Afirka," in ji Christian Schuchardt magajin garin Würzburg . ya ce "a wadannan lokutta na siyasa masu rikitarwa, wannan na da muhimmanci fiye da da."
Al'adar iyali na kowace shekara
Ga 'yan Afirka da yawa da suke zaune a Jamus, bikin ya zame musu wani taron shekara-shekara. Amina, Aliya da Soraya sun shafe shekaru suna zuwa bikin da iyayensu. "Ga yara, abu ne mai kyau su ga cewa Afirka ba kawai ta kare a kan talauci da wahala ba ne, kamar yadda aka saba bayyanata," in ji mahaifiyarsu, Vijdan (dama).
Don kaunar nahiyar Afirka
Ga yawancin Jamusawa, wata dama ce ta ganin Afirka baya dga rahotannin da manyan kafofin watsa labarai ke bayarwa. "Mun kasance a nan don kaunar kade-kade da al'adun Afirka," in ji wasu ma'aurata. Abin da suka fara nakalat daga al'adun Afirka ya fito ne ta hanyar bita. Matakinsu na gaba zai zama tafiya zuwa nahiyar Afirka ita kanta.
Dinkin kayan kwalisa daga Senegal
Dinkin kayan kwalisa na da gurbi a lokacin bikin Würzburg. Mai dinkin kaya kawa a Senegal mai suna Rama Diaw na nuna jerin dinke-dinkenta a wannan bikin tun shekaru bakwai da suka wuce. Tufafinta na musamman da ke zuwa daga manyan teloli na kasarta, lamarin da ke zama hanyar samar da ayyuka da walwala.
Daga Cape Town zuwa Marrakech
Daga shayi na mintin na Moroko zuwa ga sassake-sassaken Shona, dag gumaka na kasar Togo gami da sarka na kabilar Masai da ke kasar Kenya: Wannan balaguru ne a cikin nahiyar nahiyar cikin kimanin awa daya a Würzburg. Tantuna akalla 70 na abinci da sauran abubuwa ne ke jan hankali kan arzikin al'ada da Afirka ke da shi.
Stories and stunts
Adessa, kungiyar 'yan wasan rawa da barkwanci ta kasar Ghana suna nuna basirarsu don jin dadin mahalarta. Suna yin lankwashe-lankwashe, tare da sarkafa junansu, kuma suna raka kananan maziyarta bikin zuwa cikin dakin da aka ware wa yara. A nan ne ma, Ibrahima Ibrahima dan kasar Senegal ke jiransu, don ya nuna musu shafin yanar gizon da ya kunshi al'adun yankin Afirka ta Yamma.