1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biano a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar

August 9, 2022

Duk shekara a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar ana biki da ya daukin hankali na Biano inda mutane daga sassan kasar da ma kasashe makwabta ke halarta.

https://p.dw.com/p/4FKEv
Nomadenfest Cure Salee im Niger
Hoto: DW

A kowace shekara a birnin Agadez da ke Jamhuriyar Nijar ake bukin gargajiya na Biano, bikin da ya yi shekaru aru-aru ana gudanar da shi, inda shugabanin tsare-tsaren Biano a karkashin jagorancin mai martata sarkin abzin, bayan tsara wannan buki mai tarihi a Abzin sukan yi kira da babar murya ga matassa na su rike wannan al'ada da muhimmancin ganin yada al'adun.

Biano dai ana soma buga shi sati daya bayan salar layya inda yamma da ta kasance mafarin Biano, ke kwana uku suna bugawa, sannan kuma 'yan gabas su fara bugawa, sai kamawar sabon wata idan ya yi kwana takwas a wannan rana ce ake soma bikin inda ake kiran ranar farkon bikin da maraicin ado, inda ake ma samari maraya ado a cikin kaya na gargajiya.

Matasa dai su ne kashin bayan duk wata al'uma kuma rike al'ada wajibi ne a gare su a cewar wasu daga cikin wadanda uska halarci bikin na bana.