1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Bikin baje kolin hotuna

Gazali Abdou Tasawa SB
July 2, 2024

Cibiyar raya al'adu ta kasar Jamus ta Goethe Institut da ke Jamhuriyar Nijar, ta bude bikin baje kolin wasu hotuna da ke nuni da yanayin muhalli ke ciki a kasashen Sahel.

https://p.dw.com/p/4hmxJ
Cibiyar raya al'adu ta Jamus ta Goethe Institut
Cibiyar raya al'adu ta kasar Jamus ta Goethe InstitutHoto: DW

A Jamhuriyar Nijar kungiyar raya al'adu ta kasar Jamus ta Goethe Institut, ta bude bikin baje kolin wasu hotuna. Makasudin shirin shi ne amfani da wadannan hotuna da wasu matasan kasashen Sahel da kungiyar ta Goethe Institut ta bai wa horo fasahar yin hoto suka dauka, domin fadakar da al'ummar girman matsalar gurbatar muhalli a kasashen yankin da kuma bukatar daukar matakan tsarkake shi.

Karin Bayani: 

Yanayin Sahara na Sahel
Yanayin Sahara na SahelHoto: Zohra Bensemra/Reuters

Matsalar sauyin yanayi da gurbatar muhalli na daga cikin matsalolin da ke yin illa ga rayuwar al'umma a kasashen Sahel da dama. Domin taimaka w aga fadakar da al'ummar yankin girman wannan matsala ce da bukatar daukar matakan tunkarar ta, kungiyar raya al'adu ta kasar Jamus ta Goethe institut, ta horas da wasu matasan kasashen Jamhuriyar Nijar, Mali Burkina Faso, moritaniya da Chadi fasahar daukar hotuna ta yadda ta hanyar hotunan za su iya jan hankali jama'a da kuma fadakar da su a game da girman wannan matsala ta gurbatar muhalli a kasashen na Sahel, matsalar da ke zama dalilin mafi yawancin matsaloli na tsaro da zamantakewa da ma tattalin arziki da ke addabar kasashen.

Tarin ‘yan kallo ne dai suka halarci bikin baje kolin hotunan wadanda ke nuna irin yadda shara leda da ruwan kwatami da sauran datti suka mamaye muhallin gidaje da unguwanni a garuruwa da dama na kasashen Yankin na Sahel. Shi ma dai jakadan Jamus a Nijar Mista Olivier Schnakenberg ya bayyana gamsuwarsa da wannan baje kolin na hotuna. Za a dai share tsawon mako daya ana gudanar da baje kolin hotuna na ankarar da al'umma Nijar girman matsalar gurbatar muhalli a Sahel, bikin da za a gudanar da irinsa a sauran kasashen na Sahel a nan gaba.