Bikin al´adu na Eyo a Legas
May 15, 2009Talla
A bisa tarihi dai birnin Legas dake zama cibiyar hada-hadar kasuwanci a tarayyar Najeriya, ya samo asali ne daga wani suna EKO, wanda ake nufin "gonar rogo". Kuma a bisa al´ada Bayarben mutum ya kan fifita al´adarsa da duk wata irin al´ada da ba ta sa ba. A kan haka ne a shekaru aruru da suka shuɗe Yarbawa a Legas suke gudanar da wata al´adamda sukemkira da EYO Festival wato bikin al´adun gargajiya na EYO, wanda ke da nasaba da yin fice ta fannin rayuwa.
A kan gudanar da bikin ne domin tunawa da wani gwarzo namiji ko mace wanda ya ba da gudunmawa ta musamman ga rayuwar ´yan´uwa da ke faɗin jihar Legas baki ɗaya.
Bikin na wannan shekara ma kamar yadda aka saba ya ƙayatar ƙwarai da gaske.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed