1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Biden ya bukaci kawo karshen yakin Sudan cikin hanzari

September 18, 2024

Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci bangarorin da ke gwabza yaki a Sudan dasu gaggauta tsagaita bude wuta a yakin da aka shafe shekara daya da rabi ana yi a kasar ta Sudan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

https://p.dw.com/p/4kkBC
Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe BidenHoto: Jose Luis Magana/AP Photo/picture alliance

A wata sanarwa da shugaban ya fitar, ya ce yakin na Sudan ya dagula al'amuran shigar da kayan agajin jin kai da kuma ke kasancewa mafi muni a al'amuran da suka shafi agajin gaggawa a duniya. Kazalika yakin ya jefe rayuwar mata da kananan yara cikin tsaka mai wuya da ke fuskantar barazanar 'yunwa da fyade kusan a kowacce rana.

Karin bayani: RSF ta halaka fararen hula da dama a Sudan

Biden ya bukaci warware takaddamar da ke tsakanin shugaban rundunar sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa kuma shugaban rundunar kar-ta-kwana ta RSF Mohamed Hamdan Daglo da suka raba gari tun a watan Afrilun shekara ta 2023.