1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar mamayen Ukraine a bangaren Rasha

Zainab Mohammed Abubakar
February 19, 2022

A yayin da kwararru ke ci gaba da mahawara kan tsaro a birnin Munich na Jamus, mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta jaddada hadin kan Turai.

https://p.dw.com/p/47H6A
Münchner Sicherheitskonferenz MSC
Kamala Harris da Jens Stoltenberg a taron tsaro na MunichHoto: Andrew Harnik/REUTERS

Ana saran jawabin Kamala Harris a zauren taron a yau, ya mayar da hankali kan gargadin Rasha dangane da fuskantar mummuna kalubalen tattali idan har ta afkawa Ukraine da karfin soji.

Jawabin Madam Harris a taron shekara shekarar dai, na zuwa ne yini guda bayan da shugaba Joe Biden na Amurka ya hakikance cewar, shugaba Vladimir Putin ya shirya kai mamaya a Ukraine.

Mataimakiyar shugaban Amurkan zata yi kokarin nunar da cewar, kasashen yammaci na Turai nada rawar takawa ta hanyar hadaka, kuma mamayen Rasha na nufin gayyatar kungiyar hadakar tsaro ta NATO zuwa kofarta.

Rahotanni na nuni da cewar, a daidai lokacin da shugaban kasar Ukraine ya nufi Turai don neman dauki, shugaban Rasha zai halarci wani atisaye da sojojin kasar za su gudanar a yau a kusa da kan iyakar Ukraine, inda suka yi sansani.