1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Nukiliya: Amirka za ta zauna da Koriya ta Arewa

May 22, 2021

Shugaban Amirka Joe Biden da Shugaban Koriya ta Kudu  Moon Jae-in sun sake yin wani sabon hobbasa na ganin sun tattauna da Koriya ta Arewa a kan batun makaman nukiliyarta.

https://p.dw.com/p/3tnzD
USA PK Moon Jae-in und Joe Biden
Hoto: Jonathan Ernst/REUTERS

A ziyarar da  Moon Jae-in ya kai wa Shugaba Biden ta ranar Jumma'a a Fadar White House, Shugaba Biden ya ce zai iya ganawa da Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa idan har dama ta samu, kamar yadda yake cewa


Idan har Shugaban Koriya ta Arewan ya nuna alamun zai bada damar a tattauna da shi ni ma zan zauna da shi, amma dole sai ya amince cewa za mu yi magana ne a kan makamansa na nukiliya da kuma yadda za mu kawar da makaman.'' inji Biden

 

A jawabin da Shugaba Moon Jae-in ya yi a zantawarsa da Biden din ya ce a yanzu duniya na murna da yadda Amirka ta mayar da hankalinta ga muhimman abubuwan da ke faruwa a kasa da kasa. 

Wannan ne dai karo na biyu da Shugaba Joe Biden ya gana da wani shugaban ketare gaba-da-gaba tun bayan da ya hau mulkin Amirka a sakamakon halin da ake ciki  na coronavirus.