1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Biden: Kudade sun kusa yanke wa Ukraine

Abdullahi Tanko Bala
December 5, 2023

Fadar Shugaban Amurka ta ja hankalin majalisar dokoki cewa rashin amincewa da tallafin kudi ga Ukraine na iya bai wa Rasha nassara a yakin da ta yi da Ukraine

https://p.dw.com/p/4ZmuC
Wani sojan Ukraine a fagen yaki
Wani sojan Ukraine a fagen yakiHoto: Ozge Elif Kizil/AA/picture alliance

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce lokaci na kurewa kuma kudi na dab da yankewa na taimaka wa Ukraine a yakin da ta ke yi da mamayen da Rasha ta yi mata.

A cewar fadar ta White House matukar majalisar dokoki ba ta amince da kunshin tallafin da ta ke nema don tallafa wa Ukraine ba, to kuwa zai iya haifar da nakasu a yakin da Ukraine din ke yi da Rasha.

Gwamnatin Joe Biden ta gabatar wa majalisar dokokin Amurka bukatar amincewa da dala biliyan 106  don  taimaka wa Ukraine da Israila da kuma tabbatar da tsaron kan iyakoki amma 'yan Jam'iyyar Republican da ke da rinjaye a majalisar sun ki amincewa.

A cikin wata wasika da daraktar kasafin kudi ta shugaba Biden Shalanda Young ta aike wa majalisar ta nunar da cewa lokaci na kurewa na taimaka wa Ukraine.