1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Belgium za ta aikewa Ukraine jiragen sama na yaki guda 30

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 28, 2024

Firaministan na Belgium Alexander De Croo ya ce rukunin farko na jiragen zai isa Ukraine a karshen wannan shekara ta 2024

https://p.dw.com/p/4gNoa
Hoto: Piroschka Van De Wouw/REUTERS

Kasar Belgium za ta aike wa Ukraine jiragen sama na yaki guda 30 samfurin F-16 fighter jets, daga nan zuwa shekarar 2028, a wani bangare na yarjejeniyar tsaro da kasashen biyu suka sanyawa hannu a Talatar nan a birnin Brussels.

Karin bayani:Spain za ta ba wa Ukraine manyan makaman yaki

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky tare da firaministan Belgium Alexander De Croo sun yi maraba da wannan yarjejeniyar tsaro ta shekaru 10, da ta hada da kudi sama da Dala biliyan daya ta Amurka da Belgium za ta bai wa Ukraine a matsayin tallafin karfafa mata gwiwar kare kanta daga mamayar da Rasha ke mata.

Karin bayani:Ukraine: Taimakon Amurka na tafe

Firaministan na Belgium Alexander De Croo ya ce rukunin farko na jiragen zai isa Ukraine a karshen wannan shekara ta 2024.