1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Belarus: Rasha za ta taimaka

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 15, 2020

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun bayyana cewa suna da tabbacin kawo karshen duk matsalolin da Belarus din ke ciki nan ba da jimawa ba.

https://p.dw.com/p/3h0yZ
Belarus Minsk Lukaschenko und Putin (R)
Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko da takwaransa Vladimir Putin na RashaHoto: picture-alliance/AP Photo/T. Zenkovich

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin ta fitar, jim kadan bayan tattaunawa ta wayar tarho da shugabannin kasashen biyu suka yi kan rikicin. A hannu guda kuma 'yan adawa a Belarus din na ci gaba da yin matsin lama ga Shugaba Lukashenko ta hanyar ci gaba da yin zanga-zanga a birnin Minsk da ke zaman fadar gwamnatin kasar, abin da rahotanni suka bayyana cewa ya tilasta masa neman agajin Rasha kan batun, adaidai lokacin kuma da kungiyar Tarayyar Turai EU, ta sha alwashin kakabawa wadanda ta kiria da masu muzgunawa masu znag-zangar lumana takunkumi.