1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ganawar Bazoum da Buhari a Abuja

April 1, 2022

Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya tattauna da shugaban Najeriya a kan matsalar tsaro da samar wa da talakawa saukin rayuwa. Bazoum ya kuma gode wa jihar Zamfara da ta bai wa Nijar tallafin motocin jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/49Iwi
Nigeria | Treffen  in Abuja
Hoto: SUNDAY AGHAEZE

Kasa da sa'o'i biyu shugaba Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar mai shekaru 62 ya kwashe a birnin Abuja na Najeriya yana tattaunawa da takwaransa Shugaba Muhammadu Buhari. 


Batutuwa da daman gaske kama daga nasarar Rundunar Hada-Gwiwar Tafkin Chadi da ke yakar Kungiyar Boko Haram mai ikirarin jihadi zuwa ga ginin layin dogon da ya hade Kano da Maradi sannan kuma da wani bututun iskar gas ne dai shugabannin suka tattauna. 


“Aikin layin dogon Kano zuwa Maradi zai hade tattalin arzikin Najeriya da Nijar. Ina mika godiyata ga Shugaba Buhari domin ganin aikin ya fara, ina kuma fatan za a kamalla shi. Wannan aiki zai sauya da dama ga batun ciniki da kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.” inji Shugaba Bazoum

Nigeria | Treffen  in Abuja
Hoto: SUNDAY AGHAEZE

Duk da banbanci na mulki na mallaka dai kasashen guda biyu na kallon tsohuwar al'adar da ta hade su maimakon Turawan da suka kai ga mulkinsu a baya. 


Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya shaida wa DW cewa duk da ziyarar shugaban Nijar din ba ta yi tsawo ba, amma Najeriya ta yi masa babbar tarba. Ya kara da cewa, ziyara irin wanann dama ce ga shugabannin kasashen da ke makwabtaka da juna su tattauna abubuwan da suka shafe su gaba daya.

Ko bayan batun na tattali na arziki dai kasashen guda biyu na aiki tare a wurin kawo zaman lafiya a yankin Tafkin Chadi ya zuwa arewa maso yammacin Najeriya da nufin tunkarar matsalar rashin tsaron da ke neman tarewa a kasashen biyu.

 

Nigeria | Treffen  in Abuja
Hoto: SUNDAY AGHAEZE

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle na cikin wadanda suka gana da Shugaba Bazoum na Nijar. Shugaban Nijar ya yi amfani da ziyarar, inda ya gode wa jihar Zamfara a kan kyautar motocin da gwamnatin ta Gusau ta ba Nijar a cikin watan Maris domin sintiri a iyakoki na kasashen biyu.  

“Wannan tsaro da muke nema ba wai Najeriya ba ne kawai, abu ne da ya shafi Najeriya da Niger. Domin ana shigo da makamai daga Niger ana shiga dasu daga Najeriya. Dole mu gwamnoni sai mun taimaka wa jami'an tsaro na Nijer domin su samu karfin gwiwar dakile duk wadannan makamai da ke shigowa.'' inji Gwamna Matawalle na Zamfara.