1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayern da sha da kyar a hannun M'gladbach

Mouhamadou Awal Balarabe
August 29, 2022

Kungiyar Manchester United ta sayo dan wasan gaba Anthony daga Ajax Amsterdam a kan kudi euro miliyan 100

https://p.dw.com/p/4GC0X
Bundesliga | Bayer Leverkusen - Borussia Mönchengladbach
Hoto: Treese/nordphoto GmbH/picture alliance

Bayern Munich ta kwaci kanta da kyar a hannun Mönchengladbach yayin da Union Berlin ta yi wa Schalke kaca-kaca a mako na hudu na Bundesliga

A daidai lokacin da ya rage kwanaki uku a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa, Manchester United ta amince da farashin da zai kai kusan fam miliyan 85 kwatankwacin Euro miliyan 100 don sayen dan wasan gaba dan asalin Brazil Antony daga Ajax Amsterdam. Shi dai Antony mai shekaru 22, ya zama dan wasa na biyu da zai bi sahun kocin kungiyar Erik ten Hag, wanda ya bar lig na kasar Holland ya koma Premier League, baya ga dan wasan baya Lisandro Martinez.

Fußball Bundesliga | FC Bayern München vs. Borussia Mönchengladbach | Deutscher Meister
Kungiyar Bayern München a karawarsu da Borussia MönchengladbachHoto: Matthias Schrader/AFP/Getty Images

A Jimilace dai, manyan kamu hudu Man U. ta yi a wannan bazarar, inda ta yi nasarar sayo Tyrell Malacia da Martinez da Christian Eriksen da Casemiro. Sannan Erik ten Hag na ci gaba da fatan soyo Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon daga Barcelona tare da rike Cristiano Ronaldo duk da sha’awar da dan kasar Portugal din ke da shi na barin United domin komawa Chelsea.

Sai dai wasu kungiyoyi na kasashen Turai na ci gaba da tayin 'yan wasan da suke so a daidai lokacin da aski ke isowa gaban goshi game da cinikin 'yan wasa. Hasali ma Sofiane Diop na Monacon Faransa ya yi na'am da tayin da Nice ta yi masa na sayen shi a kan kudi Euro miliyan 22.

Shi ma Alvaro Gonzalez dan wasan baya na kasar Sipaniya ya sami sabuwar kungiya, inda ya kulla yarjejeniyar shekara guda da Al Nassr ta kasar Saudiyya karkashin jagorancin tsohon kocin Marseille Rudi Garcia. Dama Alvaro Gonzalez ya kare kwantaraginsa da Olypique Marseille ta Faransa, don haka ya isa Saudiyya a kyauta bayan rashin nasarar tuntuba da wasu kungiyoyin kwallon kafar Turkiyya da Sipaniya suka yi masa.

Italien Rom | UEFA EURO 2020 | Italien vs Wales | Andrea Belotti
Dan wasa Andrea BelottiHoto: Alessandra Tarantino/AP/picture alliance

A Italiya kuwa, AS Roma ta kulla yarjejeniyar kakar wasanni daya da Andrea Belotti da ke zama tsohon dan wasan Torino. Daraktan wasannin Roma Tiago Pinto ya ce "Andrea yana daya daga cikin 'yan wasan gaba da aka fi ji da su a gasar Seria A." Sannan ya kara da cewa "kudurinsa na zabar AS Roma ya burge mu."

Rundunar 'yan sanda Kasar Faransa ta sanar da fara bincike bayan da fitaccen dan wasanta Paul Pogba ya yi ikirarin fuskantar barazana da yunkurin kwace daga masu aikata laifi bisa hadin kan dan uwansa Mathias Pogba. Dama dai dan kwallon Juventus ya ce ya kai rahoto ga jami'an tsaro, a wata sanarwa da lauyan Paul Pogba ya wallafa.

Mathias da ke zama wa ga Paul Pogba wanda shi ma dan kwallo ne ya fitar da wani faifan bidiyo a kafar sada zumunta inda ya yi alkawarin fasa kwai dangane da wasu zafafan bayanai kan tsohon dan kwallon kungiyar Manchester United.

Shi dai Paul Pogba, wanda a halin yanzu yake jinya saboda rauni a gwiwar dama, ya tabbatar wa masu binciken cewa an yi masa barazana sau da yawa a Manchester da kuma a cibiyar samun horo ta Juventus. Ya ce ya gane dan uwansa Mathias daga cikin wadanda yake zargi da yi masa barazana.

Kasar Sipaniya ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekara 20 a ranar Lahadi bayan ta doke Japan da ci 3-1, lamarin da ke zama ramuwar gayya ta wasan karshe da Japan ta lashe a Faransa a 2018.  Godiya ta tabbata ga Inma Gabarro – 'yar wasan da ta ci kwallon farko a wasan na karshe, kuma ta fi zura kwallaye da ma gasar ta kasar Costa Rica ta dauki bakunci, inda ta tashi da kwallaye takwas a wasanni shida – sai kuma Salma Paralluelo da ta zura sauran kwallayen biyu. Amma Suzu Amano ta rage tazarar da Japan ta samu minti biyu bayan dawowa hutun rabin lokaci.

Wannan dai shi ne karon farko da Sipaniya ta lashe kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20, saboda haka take tafiya kafada da kafada a bajinta da Japan. Amma dai Koriya ta Arewa ta kasance a matsayi na biyu na yawan cin wannan kofi tun da biyu a hannunta, Yayin da Jamus  da Amirka suka kasance a sahun farko da kofi uku kowaccensu. Sai dai sakamakon yadda Brazil ta lallasa Holland da ci 4-1 a wasan neman matsayi ya sa samun matsayi na uku a gasar ta mata.

Yanzu kuma sai mu zo nan gida Jamus, inda da jibin goshi Bayern Munich ta yi kunnen doki 1-1 a gidan Allianz Arena da Borussia Monchengladbach a ranar asabar a rana ta 4 ta gasar Bundesliga. Duk da tsananin rinjaye da suka samu a farkon wasa, amma Yaya-babba ta dibi kwallo a raga kafin a tafi hutun rabin lokaci daga Marcus Thuram. Amma dai bajintar da mai tsaron gidan Bayern wato Yahn Sommer ya nuna a duk tsawon wasan, ya sa zakarun kwallon Jamus sau 10 a jere amfani da kuskuren da Borussia Monchengladbach ta yi wajen cin kwallo a cikin mintuna goma na karshe. Wannan sakamakon ya bai wa Bayern damar sake samun matsayi na farko a teburin Bundesliga da maki 10. Ita kuwa Union Berlin tana a matsayi na biyu ita ma da maki goma bayan da ta yi wa Schalke 04 dukan fitar arziki 6-1.

A sauran wasanni na Bundesliga kuwa,  Eintracht Frankfurt ta samu nasara a kan Werder Bremen da ci 4-3, yayin da Leipzig ta doke Wolfsburg da 2-0, ita kuwa Bayer Leverkusen ta yi wa Mainz cin kaca 3-0. Sai dai FC FC Köln da Stuttgart sun tasha ba wanda ya ci wani 0-0, yayin da Dortmund ta yi nasara a kan Hertha Berlin da ci 1-0.

Wimbledon | Serena Williams vs Tan
'Yar wasan tennis Serena WilliamsHoto: Takuya Matsumoto/The Yomiuri Shimbun/AP/picture alliance

Ranar farko ta gasar US Open ta tennis za ta kai kololuwarta da daren wannan Litinin, inda Serena Williams ta Amirka za ta kalubalanci 'yar Montenegro Danka Kovinic. sai dai idan ba ta yi nasara ba, wasan zai iya zama na karshe a rayuwarta. Amma dai Serena da ta lashe Grand Slam 23, za ta ci gaba a gasar mata biyu da kanwarta Venus Williams.

A rukunin maza kuwa, Daniil Medvedev da ya lashe gasar US Open da ta gabata zai yaye kallabin wasanninsa ne da fuskantar Stefan Kozlov dan Amirka. Amma Novak Djokovic ba ya halartzar gasar saboda ba a yi masa allurar rigakafi coronavirus ba. Shi kuwa dan kasar Australiya Nick Kyrgios zai yi wasansa ne da dan kasarsa Thanasi Kokkinakis.

Daga cikin wadanda idanu ke kansu a US Open dai har da dan Girkai Stefanos Tsitsipas da dan Kanada Felix Auger-Aliassime da dan Amirka Taylor Fritz.

A fannin Golf, Rory McIlroy ya lashe gasar cin kofin FedEx karo na uku a ranar Lahadi, bayan da ya samu nasarar cike gibin bugu uku da ke tsakaninsa da Scottie Scheffler lamba daya na duniya. Shi dan Irlanda ta Arewa mai shekaru 33, wanda ya taba lashe muhimman gasanni gulf sau hudu a tarihinsa, ya samu kyautar dala miliyan 18 a kusa da Atlanta, lamarin da ya ba shi damar yi  wa wanda ya lashe Masters na karshe zarra. 

McIlroy, ya kasance daya daga cikin manyan masu kare gasar PGA ta Amirka, a adawar da yake yi da yakin da kungiyar golf LIV da ke samun tallafin Saudiyya da ta raba gari da babbar gasar gof ta kasar.