1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batutuwan da suka dau hankalin jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal AH
June 30, 2017

Batun yaki da kwararar bakin haure ta Sahara da yawan 'yan gudun hijirar SWudan ta Kudu a kasarYuganda sun dau hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2fhhF
Niger  Migranten Flüchtlinge Wüste
Hoto: picture alliance/dpa/D.von Trotha

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus kan nahiyar Afirka da jaridar Die Tageszeitung wadda a wannan makon ta leka Jamhuriyar Nijar tana mai cewa:

Nijar na daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, ita ce kuma wani wurin yada zango mafi muhimmanci a Sahara ga bakin haure masu sha'awar zuwa Turai ta barauniyar hanya, suna kuma fadawa hannun miyagu masu fataucin dan Adam. Saboda haka ne yanzu gamaiyar kasa da kasa ke tallafa mata da miliyoyin dala don yaki da masu fataucin dan Adam din. Gamaiyar kasashen duniya ta kafa sansanonin karba tare da ba da shawara ga bakin haure da ake kora daga kasar Libiya. Tarayyar Turai kuma ta ba da kudin gina wata cibiyar sauke bakin haure a Agadez a wani mataki na dakile kwararar bakin haure zuwa Turai. Sai dai bisa ga dukkan alamu har yanzu da jan aiki domin har kwanan gobe masu fataucin dan Adam na gudanar da haramtaccen aikinsu, lamarin kuma da ke janyo asarar rayukan mutane a Hamada. Hukumomin Agadez na korafin cewa rashin cika alkawari daga bangaren gamaiyar kasa da kasa na daga cikin abubuwan da ke kawo cikas bisa manufar yaki da masu fataucin dan Adam a yankin.

A labarin da ta buga mai taken Sabunta Nahiyar Afirka na tattare da matsaloli jaridar Neues Deutschland ta ce:

Deutschland G20 Afrika Treffen
Hoto: Getty Images/AFP/J. Macdougall

Rashin sahihan manufofin ayyukan raya kasa da matsalar cin hancin da rashawa na hana samun wani ci gaba na a zo a gani a kasashen Afirka da yawa. Jaridar ta kara da cewa nahiyar Afirka na taka muhimmiyar rawa a wa'adin shugabancin Jamus na Kungiyar kasashen G20. Saboda haka gwamnatin tarayyar Jamus ke fatan cewa zuba jari mai yawa kai tsaye a Afirka, zai karfafa gwiwa tare da ba da kyakkyawan fata. Da haka kuma za a iya rage yawan masu kwarara zuwa Turai. Sai dai a cewar jaridar kasashe masu arzikin kuma ke yi wa yunkurinsu karar tsaye, domin kayayyakin da suke ba wa Afirka a matsayin taimako su din ne kuma ke durkusar da kamfanonin kasashen Afirka.

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a wannan makon ta leka kasar Yuganda ne tana mai cewa:

Afrika Uganda - Südsudanische Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Kasar Yuganda da ke gabacin Afirka na amfani da manufofi masu sassauci dangane da ‘yan gudun hijira. Kowane dan gudun hijira a kasar ta Yuganda na da ‘yancin mallakar filin noma da ‘yancin kiwon lafiya da na ilimi. Ba wa ‘yan gudun hijirar damar yin aiki don sama wa kansu kudin shiga, yana taimaka wa tattalin arzikin yankin da suke, domin na tara wa Yugandar kudaden haraji. Sai dai hakan ka iya canjawa saboda yawa fiye da kima da ‘yan gudun hijira na Sudan ta Kudu suka yi a kasar. Yawan su kuma na barazana ga zaman lafiyar kasar. Ko da yake kasar ta ce za ta ci gaba da bude kan iyakokin ta, amma lamarin na son ya fi karfin ta. Watau a fakaice tana son ta rufe kofofin ta saboda karancin kudi. Ita kuma gamaiyar kasa da kasa ba ta taimaka wa da wani abin kirki.