1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun ceto kuɗin Euro ya gamu da cikas

October 12, 2011

Matakin 'ya'yan majalisar dokokin Silovakiya ya saka batun ceto kuɗin euro cikin rashin tabbas, inda yan majalisar suka yi watsi da batun asusun ko ta kwana.

https://p.dw.com/p/12qih
Tutocin Silovakiya da na EU a gaban majalisar dokokin ƙasarHoto: dapd

A ranar Talata majalisar dokokin ƙasar Silovakiya ta yi wasti da shirin ceto darajar kudin euro. Wannan ƙin amincewar dai koma bayane ga ƙasashen dake amfani da kudin na Euro, domin dole sai daukacin ƙasashen 17 sun amince kafin shirin ya fara aiki. Rashin amincewar dai babbar alamace ta rarrabuwar kawuna a gwamnatin haɗakan dake mulki. A yau jam'iyun za su sake ganawa don kaɗa ƙuri'a zagaye na biyu. A wani shirin da zai ceto ƙasashen da suka kasa kamar misali Girka.

Shugaban majalisar dokokin ƙasar ta Silovakiya yace wannan matakin na su ya kawo koma baya ga ɗaukacin masu biyan haraji na Turai. Ƙasashen dake amfani da euro sun tsara samar da euro biliyan 300 a matsayin asusun tallafawa duk wata ƙasa da aka ga tattalin arzikinta na tangal-tangal. Duk da cewa majalisar dokin ƙasar ta yi watsi da batun, amma gamayyar jam'iyun dake mulki suka ce za su sake tattaunawa domin yan majalisar dokokin su sake zama na biyu. Inda shugaban majalisar dokikin yace:

"Silovakiya ita ce mafe talauci cikin Tarayyar Turai. Amma duk da haka dole ta bada kudinta ga sauran ƙasashen. Batun tsarin ceto kudin euro yana fiskantar matsala a yarjejeniyar da gamayyar jam'iyun mu suka cimma, kuma adawar tana da yawa a tsakanin al'ummar Silovakiya"

Finanzkrise EU EFSF Rettungsschirm Slowakei Bratislava Richard Sulik
Zaman majalisar dokokin Silovakiya ya saka batun ceto euro cikin ruɗaniHoto: dapd

An dai yi muhawara a tsanaki a majalisar dokokin ta Silovakiya, an kuma dauki lokaci mai tsawo ana yin ta, inda 'yan majalisar suka dauki misali sa'o'i goma suna muhawara. Firai minista Iveta Radicova ta yi kira ga yayan majalisar su manta da banbancin dake tsakanin su, su kuma amince da dokar da za ta bada damar ɗaukar matakan ceto kuɗin na Euro.

"A ce wai wannan matsala ce da bata shafe mu ba, babban kuskure ne, kuma rashin ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyan mu ne. Duk gwamnatin da ta kasa maida martani ga canje-canje idan suka samu, to kuwa bata cancanci ta yi mulki ba."

An dai yi imanin cewar mafi yawan wadanda suka ki goyon bayan kudurin sun fito ne daga jam'iyar SaS, wadda ita ce kadai daga cikin jam'iyun dake hadin gwiwa a gwamnati dake kyamar matakin na ceto Euro. Hakan ya nuna cewar jam'iyar mai hadin gwiwa a gwamnati, ita ce kuma za ta zama sanadiyyar kawo karshen gwamnatin Iveta Radicova, abin da ya zama babban kaye da cin mutunci ga Firayim ministar yar jam'iyar Christian Democrats, wadda yanzu ma shekara guda kenan da take kan mulki, inda tace:

"Halin da aka shiga a yau, ya kai mu ga tambayar: shin ina Silovakia take son nufa? Shin mun fi son hadin kai ne da zumunci da daukar nauyin dake kanmu, ko kuwa mun fi bukatar ci gaba da gwagwarmayar siyasa da cin mutuncin juna ko ta halin yaya?"

A ƙarshe dai Silovakiya ta zabi gwagwarmayar siyasa maimakon hadin kai tsakanin juna. To sai dai duk da haka ba za'a gudanarda sabon zabe a kasar ba. Ganin cewar a yanzu gwamnatin dake kan mulki ta janye, yan adawa sun yi alkawarin cewar idan aka sake kai batun na ceto Euro karona biyu a majalisar za su bada goyon baya da amincewar su.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu