1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Shimfida bututun mai tsakanin Yaganda da Tanzaniya

Suleiman Babayo AMA
November 29, 2023

Kotun gabashin Afirka ta yi watsi da bukatar dakatar da shimfida bututun man fetur na karkashin kasa tsakanin Yuganda da Tanzaniya wanda zai lashe makuden kudi amma ake ganin zai iya gurbata muhalli.

https://p.dw.com/p/4Zaxb
Yarjejeniyar shimfida bututun mai | Samia Suluhu Hassan da Yoweri Museveni
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta Tanzaniya da Shugaba Yoweri Museveni na YugandaHoto: Presidential Press Unit/Uganda

Wata kotun yankin gabashin Afirka ta yi watsi da koken da aka shigar kan shimfida bututun man fetur na bilyoyin dala tsakanin kasashen Tanzaniya da Yuganda da 'yan gwagwarmaya na kare muhalli suke matukar adawa da tsarin na shimfida bututun da suke ganin zai gurbata muhalli.

Kotun ta kasashen yankin ta ce ba ta da hurumin sauraron karar da ke kalubalantar matakin na shimfida bututun man fetur. Tsarin zai lashe makuden kudi kimanin dalar Amirka milyan dubu-10 da kamfanin kasar Faransa na Total zai yi daga wuraren hakar man fetur na Yuganda zuwa wuraren gabar teku na kasar Tanzaniya.