1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBelgium

An rantsar da sabon firaministan Beljiyam

Abdourahamane Hassane
February 3, 2025

Jagoran masu ra'ayin rikau na Flemish Bart De Wever, a hukumance ya zama sabon firaministan kasar Beljiyam

https://p.dw.com/p/4pydN
Hoto: AP

 Bart De Wever ya sha  rantsuwa kama aiki a gaban sarki Philippe a fadar sarkin tare da mambobin gwamnatinsa 14.

Bart mai shekaru 54 wanda ya kwashe shekaru 12 a matsayin magajin gari na Anwert ta arewa, shi ne dan awaren Flemish na farko da ya karbi shugabancin gwamnatin tarayya a Beljiyam

Kusan watanni takwas bayan gudanar da zabukan ‘yan majalisu, wanda jam'iyyarsa ta N-VA ta samu  nasara a Flanders,

 kuma zai gudanar da mulkin  tare da jam'iyyu hudu na   kawance.