1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus kan barnar guguwar Idai

Mohammad Nasiru Awal RGB
March 29, 2019

Iftila'in guguwa da ambaliyar ruwa da ya afka wa wasu kasashe uku na yankin kudu maso Gabashin Afirka da suka hada da Mozambik da Zimbabuwe da kuma Malawi na ci gaba da daukar hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3FsdW
Mosambik Idai Zyklon
Hoto: Reuters/M. Hutchings

A labarin da ta buga mai taken "farkon ambaliya sai kuma yunwa" jaridar Die Tageszeitung ta fara da cewa a kasar Malawi daya daga cikin kasashen da guguwar da ake wa lakabi da Idai ta yi wa ta'adi, kusan albarkatun gona musamman masara sun lalace, lamarin ya daidaita rayuwar kananan manoma a kasar, inda tun kafin saukar bala'in ake fama da karancin abinci. Gwamnati ta yi alkawarin taimaka wa manoman da sabbin iri, sai dai ana rashin kudin samar da irin inji jaridar inda ta ruwaito kakakin gwamnati na cewa ana bukatar karin kudade da za a talafa wa kananan manoman da su.

A labarin da ta buga dangane da halin da ake ciki a kasashen uku na yankin Kudu masi Gabashin Afirka, jaridar Berliner Zeitng ta ce bayan da guvguwar Idai ta yi kaca-kaca da wani yanki na kasar Mozambik, yanzu cutar amai da gudawa wato Cholera ce take yaduwa. Ta ce al'ummomin kasashen Mozambik da Zimbabuwe da Malawi da suka fuskanci guguwar Idai da ambaliyar ruwa har yanzu na cikin mawuyacin hali, baya ga asarar daruruwan rayuka yanzu cutar cholera ce ta barke, inda ta fi muni a birnin Beira mai tashar jirgin ruwa a kasar Mozambik. Jaridar ta ruwaito likitoci da wasu ma'aikatan kungiyoyin agaji na nuna fargabar yiwuwar barkewar annobar wasu cututtukan kamar Typhoid da Maleriya da cututtuka da ke shafar fata da hanyoyin numfashi.

Vereinigte Arabische Emirate, Dubai - Ein kenianischer Lehrer für Naturwissenschaften gewann einen Preis im Wert von 1 Million Dollar
Malamin da ya lashe kyautar dala miliyan dayaHoto: picture-alliance/J. Gambrell

Gwamnatin tarayyar Jamus ta amince da sabuwar manufar kasa kan nahiyar Afirka inda za a mayar da hankali kan batun ci-rani da yadda za a yaki matsalar tun daga tushe injin jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Jaridar ta ce sabuwar manufar da gwamnatin ta Jamus ta amince da ita za ta kuma karfafa hadin kai da kasashen Afirka wajen samar da zaman lafiya da tsaro da kuma kwanciyar hankali inda za a kara yawan kudin da ake sakawa a fannin ci-gaban tattalin arziki da jin dadin mata da matasa. Gwamnatin Jamus na daukar kasashen Afirka da kungiyar tarayyar Afirka ta AU a matsayin manyan abokan kawance masu muhimmanci da in an hada kai za a cimma manufar da aka sa gaba.

Za mu kammala sharhin jaridun na Jamus da jaridar Die Tageszeitung wadda ta ce wani malamin makaranta a Kenya ya zama gwarzon malami na shekara a duniya. Ta ce a bana Peter Tabichi da ke zama malamin lissafi da ilimin ya ci kyautar "Global Teacher Prize" da aka yi bikin a Dubai, inda ya samu kyautar kudi dala miliyan daya. Shi dai Peter Tabichi mai shekaru 36, ya na kuma koyarwa a wata makaranta da ke yammacin kasar Kenya, ya kan kashe kashi 80 cikin 100 na albashinsa a wata wajen taimakawa yaran makarantar.