1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar Sudan ga Sudan ta kudu

April 19, 2012

Shugaban Sudan ya ce a shirye ya ke ya afka wa sudan ta kudu da yaƙi domin kawar da takwaransa Salva kir daga karagar mulki. Sai dai ƙasashen duniya na nuna damuwa.

https://p.dw.com/p/14gp9
** FILE ** In this Friday, Sept. 14, 2007 file photo, Sudanese President Omar al-Bashir is seen in Rome, Italy. Prosecutor Luis Moreno-Ocampo asked a three-judge panel at the International Criminal Court to issue an arrest warrant for President Omar al-Bashir on genocide charges Monday July, 14, 2008, accusing him of masterminding attempts to wipe out African tribes in Darfur with a campaign of murder, rape and deportation. (AP Photo/Gregorio Borgia, File)
Hoto: AP

Shugaba Omar Hasan al-Bashir na Sudan ya yi barazanar hamɓarar da takwaran aikinsa na Sudan ta kudu, bisa dalilan da ya danganta da neman ceto al'umar ƙasar daga rikicin kan iyaka na ƙasashen biyu da ke maƙobtaka da juna. Al-Bashir ya bayyana cewar Salva Kir da ke shugabantar Sudan ta kudu tun bayyan da ta zama ƙasa mai cin gashin kanta a watan julin bara, wani ƙwaro ne da ya kamata a kawar daga karagar mulki.

Shi dai salva Kir, tsohon shugaban ƙungiyar tawaye na ta SPLM ne, da ta yi ta takun saƙa da Gwamnatin tsohuwar haɗaɗɗiyar Sudan, sakamakon zarginta da mayar da 'yan kudancin ƙasar saniyar ware. Ƙasashen biyu na taƙaddama ne da juna game da wani yankin kan iyaka mai arzikin man fetur.Faɗace faɗace sun tsananta a makwanin baya-bayannan tsakanin Sudan da kuma Sudan ta kudu.

A halin yanzu dai ƙasar Sudan ta kudu ta mamaye yankin Heglig mai arzikin man fetur kuma mallakin ƙasar Sudan. Ƙasashen duniya daban daban sun yi kira ga ɓangarorin biyu da ke gaba da juna, da kai hankali nesa tare da komawa kan teburin shawarwari domin warware rikicin na kan iyaka tsakanin Sudan da kuma Sudan ta kudu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu