1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar ricikin Siriya

March 21, 2012

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyanar da rikicin Siriya a matsayin abin da ka iya yin barazana ga duniya

https://p.dw.com/p/14OgQ
U.N. Secretary-General Ban Ki-moon (L) meets Indonesia's President Susilo Bambang Yudhoyono at the Presidential Palace in Bogor March 20, 2012. Ban said on Tuesday that the situation in Syria was unacceptable and called for the international community to speak with one voice and for Security Council members to display unity. REUTERS/Supri (INDONESIA - Tags: POLITICS)
Ban Ki-moon(a hagu) yayin ziyararsa a IndonesiyaHoto: Reuters

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya sake kira halin da ke wakana a kasar Siriya tamkar rikici mai hadarin gaske da ka iya shafar duniya ga baki dayanta. A cikin jawabin da ya yi a birnin Jakarta na kasar Indonesiya, Ban ya ce ya zamo wajibi gamayyar kasa da kasa ta dauki alhakin samun mafita daga wannan mummunan rikici, yana mai cewa hakan zai yi barazanar gaske ga wannan yanki da kuma duniya baki dayanata. Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wannan kashedin ne kwana daya bayan da komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake yunkurin samun daideto akan matsayinsa game da Siriya. To sai dai komitin ya kammala zaman taronsa ne ba tare da cimma wata matsaya ko kuma sakamako ba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi