1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan jihadi na barazana ga tsaron Burkina Faso

Ramatu Garba Baba
February 21, 2023

An tabbatar da mutuwar sojoji kimanin 51 a sakamakon wani kazamin harin kwanton bauna da ake zargin mayaka masu da'awar jihadi da kai wa kan jami'an a Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/4NmC0
Burkina Faso | Soldaten
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Alkaluma na wadanda suka mutu a sakamakon harin ta'addanci da aka kai kan rundunar sojin kasar Burkina Faso ya haura zuwa hamsin da daya, bayan da aka gano karin gawarwaki arba'in da uku a ranar Litinin din da ta gabata. Mayakan masu da'awar jihadi, ake zargi sun kai wa rundunar sojin hari irin na kwanton bauna a wani yanki mai suna Oudalan, kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar ta sheda.

Tun dai a makon jiya aka kai harin a daidai lokacin da gwamnatin Burkina Fason, ta tsaya kai da fata na ganin lallai sai sojojin Faransa kimanin dari hudu da suka yi saura a kasar sun fice. Masana tsaro a na su bangaren na ganin cewa, sabanin da aka samu a tsakanin Faransa da kasar ne ya kara bai wa mayakan masu da'awar jihadin damar cin karensu ba babbaka, wanda shi ke kara tasiri a munanan hare-haren da kasar ke fuskanta a yanzu.