1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar matsalar jin kai a kasar Nijar

Binta Aliyu Zurmi MAB
August 10, 2023

Makonni biyu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar, kungiyoyin agaji sun koka game da hauhawar farashin kayan abinci. Kungiyar Welthungerhilfe ta Jamus ta yi gargadi kan barazanar fadawa cikin matsalar jin kai.

https://p.dw.com/p/4UzJH
Coup aftermath in Niger
Hoto: Sam Mednick/AP/picture alliance

Kungiyar Welthungerhilfe ta kasar Jamus ta ruwaito cewa farashin buhun shinkafa ya tashi da kashi 50 cikin 100, sannan man fetur ya kara tsada da kashi 20 cikin dari. 

Shugaban kungiyar ta agajin Jameson Gadzirai ya shaida wa kafafen yada labarai na Jamus cewa bukatar taimakon jin kai zai iya karuwa a Nijar, kuma halin da jama'a ke ciki zai iya kaiwa ga matakin barazanar karancin abinci. 

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ke neman mafita kan halin da ake ciki a Nijar a wani taron koli da suke gudanarwa a Abuja babban birnin Najeriya.