Burkina Faso: Fulani na cikin fargaba
August 18, 2022Gwamnatin Burkina Faso ta yi tir da kiraye-kiraye a kafofin sada zumunta, na hada kai domin kai hari kan tsirarun Fulani da ke zaune a kasar, gwamnatin ta kwatanta matakin da wani yunkurin mai kama da rikicin kabilanci mafi muni da aka aikata a kasar Ruwanda. Kakakin gwamnati Lionel Bilgo ya ce, sautin kira na aikata wannan ta'asa da aka yada ta manhajar Whatsapp, na dauke da kalamai masu muni da hadari, inda ya gargadi 'yan kasar da kada su bi son zuciya a tayar da zaune tsaye.
Tuni gwamnati ta nemi taimakon malaman addinai da sarakunan gargajiya dama duk masu fada a ji, kan su taimaka wajen kwantar da wannan kurar. Yunkurin kai hari kan Fulanin ya soma ne, bayan tarin zarge-zarge da ake yi musu na zama mayakan jihadi, na baya-bayan nan, shi ne wani hari da aka zargi Fulanin da kai wa a kauyen Yirgou da ke arewacin kasar, mutum shida suka mutu ciki har da mai unguwa kuma a harin ramuwar gayya aka halaka Fulanin da suka kasance 'yan tsiraru kimanin hamsin.