1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a gwamnatin Jamus kan 'yan gudun hijira

Gazali Abdou Tasawa
June 18, 2018

Jam'iyyar CSU mai kawancen da CDU a Jamus ta bai wa shugabar gwamnati Angela Merkel wa'adin makonni biyu ta yi watsi da siyasarta ta karbar 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2zmkm
Horst Seehofer und Kanzlerin Merkel
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Schreiber

A kasar Jamus, gwamnatin Angela Merkel na tangal tangal a sakamakon kalubalen da take fuskanta daga abokiyar kawancanta ta CSU kan batun 'yan gudun hijira inda yanzu haka jam'iyyar ta CSU ta bayar da wa'adin makonni biyu ga shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel kan ta yi watsi da siyasarta da karbar 'yan gudun hijira a cikin kasar da kuma gaggauta samun daidaito da kasashen Turai kan wannan batu.

Jam'iyyar ta CSU wacce ke kawance da jam'iyyar CDU tun a shekara ta 1949 ta na bukatar ganin daga yanzu gwamnatin kasar ta dauki matakin korar daga cikin kasar ta Jamus, illahirin 'yan gudun hijirar da aka rigaya aka yi rijistansu a wata kasa ta Turai. 

Matakin da shugabar gwamnatin ta Jamus ta ki lamunta da shi tana mai cewa bai dace ba Jamus ta yi gaban kanta cikin wannan matsala ta 'yan gudun hijira wacce kasashen Turai ke kokarin samar mata da mataki na bai daya.