1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin duniya zata sa fifiko wajen raya nahiyar Afrika

Zainab A MohammadOctober 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvSc
Hoto: AP

Raya cigaban kasashen nahiyar Afrika,zai kasance batu da Bankin duniya zatafi mayar da hankali akai cikin ayyukanta na raya kasashen duniya.

Kasa da watanni shida da hayewa kujerana shugabancin bankin duniya,Mr Poul Wolforwitz ya sanar da fifikonsa wajen shawo kan matsaloli na talauci da sauran matsaloli dake addabar nahiyar Afrika.

Ya fadawa yan majalisar ayyukan bankin duniya a Finland cewa,abun takaici ne halin da kasashen yankin sahara na Afrika ke ciki a yanzu haka.

To saidai shugaban bankin duniya ya kara dacewa bazaar cimma tudun dafawa a wannan yunkuri da bankin keyi ,idan har alummomi da shugabannin kasashen Afrikan basu bada hadin kai ba domin cimma wannan buri.

Yace matsalolin dake addabar nahiyar Afrika,ba batu ne da Bankin duniya da kasashen duniya zasu iya shawo kansu su kadai ba,dole ne Shugabannin kasashen suyi nuni dacewa a shirye suke su kalubalanci matsalar talauci dake addabansu.

Daya ke amsa tambayoyin yan majalisar bankin dake wakiltan sama da kasashe 110,Mr Wolfowitz yace Bankin zai mayar da hankali wajen samarda kayayyakin more rayuwa a Afrika,wadanda zasu taimaka inganta tattalin arzikinta.

Ya lissafta ayyukan cibiyar samarda wutan lantarki a kudancin Afrika,wanda zai samarwa kasashen janhuriyar democradiyar Congo da Malawi da Zimbabwe da Afrika ta kudu,ingantaccen wutan lantarki.Bugu da Karin Bankin duniyan na kuma shirin daukan nauyin gudanarda gyaran manyan hanyoyi daga yankunan tekun India zuwa Na Atlantika.

Wani muhimmin aiki da bankin duniyan ke gudanarwa tare da hadin gwiwan manyan kamfanonin mai,batu kuma dake fuskantar adawa daga kungiyoyin kare muhalli da kewayen dan adam,shine gyaran bututun man gas a yankin yammacin Afrika,wanda idan aka cimma kammalashi,man gas zai kwarara kai tsaye daga Nigeria zuwa janhuriyar Benin,kana daga Togo zuwa Ghana.

To sai dai shugaban Bankin duniyan ya tunatar dacewa,mayar da hankali kan wadannan ayyukan na inganta rayuwa bazai sa bankin yayi watsi da ayyukan inganta lafiya da harkoki na ilimi dake gudana a halin yanzu a Afrika ba.

Kazalika Mr Wolfowitz yayi kira ga kasashe masu cigaban masanaantu dasu cikanbta alkawura da suka dauka na yafewa kasashe matalauta basussukan da suke binsu.

Yace baya ga haka ,dole ne su tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma adangane da cinikayya a birnin doha,domin hakan ne kadai zain inganta rayuwan mutane billion 1 da digo 2 ,dake rayuwa a kasa da Dala guda a kowane yini a kewayen duniya.

Yarjejeniyar doha da aka kaddamar a shekara ta 2001,a karkashin kungiyar cinikayya ta duniya ,nada nufin bunkasa tattalin arzikin duniya tare da cire miliyoyin mutane daga kangin talauci.

Wannan gabatarwa da shugaban Bankin duniya Wolfowitz yayi a gaban yan majalisar dokokin kasashe daban daban dai,wanda kuma ke zama na farkon irinsa tun daya haye wannan mukami,ya bashi daman karyata jite jiten da ake yadawa lokacin nadinsa, nacewa bashi da wata masaniya dangane da harkokin gudanarwa da suka danganci raya cigaba.