1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Somaliya ta samu rancen kudade

Suleiman Babayo AS
September 26, 2018

A karon farko cikin shekaru 30 da suka gabata kasar Somaliya mai fama da tashe-tashen hankula ta samu rance kudade kimanin Dala milyan 80 daga Bankin Duniya.

https://p.dw.com/p/35XRF
Anschlag in Mogadischu
Hoto: Reuters/Munasar Mohamed

Bankin Duniya ya amince da bayar da bashin kudade kimanin dalar Amirka milyan 80 ga kasar Somaliya domin inganta tsarin tattalin arzikin kasar, lamarin da ke zama na farko a shekaru 30 da suka gabata ga kasar da yaki ya galabaita, kamar yadda bankin ya tabbatar.

A baya Bankin Duniya ya katse hulda da Somaliya bayan barkewar yakin basasa a shekarar 1991, amma aka koma taimakon kasar a shekara ta 2003 lokacin da aka mayar da hankali kan magance cutar AIDS da inganta kiwo.

Bisa matakin da ake dauka ana sa ran kasar ta Somaliya za ta samu bunkasa na tattalin arziki da kashi 3.5 zuwa kashi 4.5 cikin 100 daga shekara ta 2019 zuwa shekara ta 2022.