1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin duniya da matsayin noma a kasashe matasa

Umaru AliyuNovember 6, 2007

Bankin duniya ya gabatar da rahoton na shekara a game da matsayin noma a kasashe ma su tasowa

https://p.dw.com/p/C4nn
Minista Wieczorek-Zeul da shugaban Bankin Duniya Zoellick a BerlinHoto: AP

Ministan taimakon kasashen ketare ta Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul ta tabbatar da goyon bayan ta ga matsayin bankin duniya ga aiyukan noma a fannin raya kasashe masu tasowa. Minista Wieczorek-Zeul ta fadi a Berlin cewar rahoton raya kasashen ketare da bankin duniya ya gabatar a watan Oktoba ya nuna cewar ana bukatar kawo karshen babakeren da manyan kasashe masu ci gaban masana’antu suke yi wa kayaiyakin albarkatun gona daga kasashe masu tasowa. Hakan zai baiwa kananan kasashen cikakkiyar dama ta shigar da kayaiyakin su zuwa kasuwannin kasashe masu ci gaban masana’antu.

A rahoton da su ka gabatar cikin watan Oktoba, masana na Bankin Duniya sun nuna cewar samun bunkasar aiyukan noma yana da matukar muhimmanci a fannin samun bunkasar tattalin arziki, kamar dai yadda zuba jari a kananan kasashen yake da muhimmanci a kokarin su na samun ci gaban tattalin arziki. Masanan suka ce wajibi ne a kara maida hankali ga fannin zuba jari a aiyukan noma, bisa manufar taimakawa kasashe masu tasowa a kokarin su na raya kasa, muddin ana bukatar cimma burin nan na Millenium, wato rage matsalar talauci da misalin kashi hamsin cikin dari nan da shekara ta 2015, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta shimfida.

Ministan taimakon raya kasashen ketare, Heidemarie Wieczorek- Zeul ta yaba da ganin cewar a cikin rahoton, bankin duniya ya bukaci gwamnatoci su dauki matakai na kare kananan manoma, saboda sune masu samar da mafi yawan kayan abinci da kasashen masu tasowa suke bukata, musamman mata, wadanda sune masu noma tsakani kashi sittin zuwa kashi tamanin cikin dari na kayan amfanin gona a kasashe masu tasowa.

Ministar ta kuma yi kira ga kasashe masu ci gaban masana’antu su gaggauta daukar matakai na rage babakere da kariyar da suke sanyawa, domin toshe kasuwannin ga kayaiyakin amfanin gona daga kasashe masu tasowa. Tace:

Ina so in nunar a fili cewar ina ganin ya kamata cikin gaggawa a kawo karshen matsalar nan da da bata da wani amfani, inda manyan kasashe suke shigar da kudade masu yawa domin taimakawa manoman su, abin dake hana manoma daga kasashe masu tasowa su shiga takara sosai da takwarorin su na manyan kasashen.

To amma tace suma kasashe na Afrika da Asiya da Latinamerika, tilas ne su shiogard a karin jari a aiyukan su na noma. Tace abin bakin ciki ne ganin cewar mafi yawan masu fama da yunwa a kasashen masu tasowa, kananan manoma ne da basa iya takara da takwarorin su na kasashe masu arziki. Rahoton bankin duniya ya nuna cewar kashi ukku cikin kashi hudu na wadanda suka fi fama da talauci a tsakanin kasashe masu tasowa, suna zaune ne a yankunan karkara, inda mafi yawan su suke rayuwa tare da abin da bai kai dolar Amirka daya ba a rana. Wannan ma babban dalili ne da zai sanya a kara maida hankali a aiyukan taimakon raya kasa zuwa ga aiyukan noma a kasashen masu tasowa. A maimakon haka, kashi hudu ne kawai cikin dari na kudaden da akan bayar a matsayin taimakon raya ake zuba su a fannin noma, duk kuwa da ganin cewar bunkasar jama’a da canjin yanayi, suna kawo barazana ga samar da isasshen abinci a kasashen masu tasowa. Minista Heidemarie Wieczorek-Zeul tace tun daga yan shekarun baya, manufofin taimakon raya kasa na Jamus suna maida hankalin su ne ga fannin bada ilimi a kasashe da suka fi fama da talauci a duniya. Wannan kuwa ba kuskure bane, inji ta.

Tace babu wani abin zabi fiye da hakan, domin kuwa baiwa jama’a ilimi yana nufin samar masu da abin yi kenan. Ana kuma iya ganin cewar noma bangare ne da mutane masu tarin yawa suke rayuwa dashi a kasashen Afirka kudu da Sahara. A duniya baki daya, kashi saba’in da biyar cikin dari na masu fama da talauci suna zaune a yankunan karkara na kasashe masu tasowa. Samar masu da aikin yi, yana nufin taimaka masu kenan da yadda za su iya tura ‚ya’yan su zuwa makaranta.