1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hasina ta kama aiki a sabon wa'adin mulki

Mohammad Nasiru Awal MAB
January 7, 2019

A Bangaldesh Firaminista Sheikh Hasina ta sha rantsuwar kama aiki a wa'adin mulki na uku a jere bayan jam'iyyarta ta Awami League ta lashe zabe.

https://p.dw.com/p/3BA1D
Sheikh Hasina
Hoto: bdnews24.com

Firaministan Bangladesh Sheikh Hasina a wannan Litinin ta sha rantsuwar kama aiki a wa'adin mulki na uku a jere a matsayin shugabar gwamnati. An kuma rantsar da da yawa daga cikin ministocinta.

Firaminista Hasina ta ci gaba a kan mukaminta bayan da jam'iyyarta ta Awami League ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki karo na 11 da gagarumin rinjaye, nasarar da jam'iyyun adawa suka yi watsi da ita sua masu korafin cewa an tursasa musu an kuma yi magudin zabe.

'Yan adawar dai sun kauracewa bikin rantsar da Firaministan inda suka ci gaba da kiran a sake gudanar da zaben.