1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar corona ta rarrabuwar kawunan kasashen Afirka.

Usman Shehu Usman AMA
August 26, 2021

Masana a kasashen Afirka ta Kudu da Kenya sun yi ittifakin cewa samar da alluran rigakafin corona a nahiyar Afirka na da banbanci da na kasashe mawadata.

https://p.dw.com/p/3zWgn
Tansania | Coronavirus | Impfungen in Dar es Salaam
Hoto: Ericky Boniphace/DW

Bullar sabon nau’in cutar COVID-19 a nahiyar Afirka, da kuma rashin dai-daito kan rabon alluran rigakafi kama daga cikin nahiyar dama a fadin duniya duk Afirka ce ta baya. Wata babbar matsalar it ace samar da rigakafin a masu bukata. Hatta ga kasashen da ke wadataccen alluran rigakafi, kamar Afirka ta Kudu, suna fiskantar kalubalen da suka hada da kin karbar alluran da mutane ke yi a bisa hujjar labaran boge da ake yadawa masu cewa riga kafin da ake bayarwa na da illah.

Mutane da yawa sun kauracewa rigakafin kamar yadda wannan da ke zama a birnin Johannesburg ya bayyana inda ya ce "Don me zan yi allurar rigakafin alhali akwai maganin gargajiya da zai warkar da cutar? Kuma kari shine naga illar allurar domin wasu da aka yiwa damtsen hannunsu da kafadunsu sun kumbura, wassunsu ma har sai da suka yi jinya." Ana matukar bukatar sahihan bayanai da za su kawar da wannan shaci-fadi da jahilci, a cewar Linda-Gail Bekker, Farfesa a bangaren magunguna da ke jami’ar Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.

Sabon nau'in corona ya yadu a Kenya

Südafrika Corona-Pandemie | Arwyp Medical Centre
Hoto: hafiek Tassiem/REUTERS

Sai dai a kasar Kenya inda sabon nau’in coronan ya yi saurin yadauwa, akwai karancin alluran rigakafin ga masu bukatar karba, hakan kuma duk irin tashin hankali da jamaa suka shiga. A Monica Wanjiku da ta rasa iyalanta uku sanadiyyar annobar ta fadi yanayin da shiga tana mai cewa "Zuciyata na cike jin zafi. Ban san ma me zan fada ba, amma ina ganin da a ce an yi wa mutanen riga kafin da sun warke."

Yayinda kasar Afirka ta Kudu ta iya yiwa mutane miliyan 10 riga kafin corona, ita kuwa kasar Kenya milyan biyu ne kawai suka iya samun allurar. Kasashen Afirka dole sai sun tsaya don magance cutar, ya yinda wasunsu ke fama da karancin magani bisa rashin kudi da suke fama da shi kasa ga kasashe mawadata, akwai matukar bukatar kara wayarda kan mutane ingancin alluar rigakafin.