1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki Moon zai ba da fifiko wajen warware rikicin Darfur

January 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuVi
Yayin da yake fara aikin sa a matsayin sakatare janar na MDD, sabon babban sakataren na gamaiyar ta kasa da kasa, Ban Ki Moon ya bayyana muhimman batutuwan da zai fi mayar da hankali kai. Ban ya fada a birnin New York cewa zai bawa kokarin warware rikicin yankin Darfur na Sudan wani fifiko na musamman. Ya ce zai tattauna da shugaban Sudan Omar Hassan al-Bashir a gun taron kolin kasashen kungiyar tarayyar Afirka da za´a yi a cikin wannan wata. Wani muhimmin batu kuma shi ne takaddamar nukiliya da ake da KTA, inji Ban. Tun daga ran daya ga watan janeru Ban mai shekaru 62 daga KTK ya karbi ragamar sakatare janar na MDD.